Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sa’ad da shekaru saba’in suka cika a Babilon, zan zo muku in cika alkawarin alherina don in komo da ku zuwa wannan wuri.
Za su zauna a can lafiya su kuma gina gidaje su nome gonakin inabi; za su zauna lafiya sa’ad da zan zartar da hukunci a kan dukan maƙwabtansu da suka wulaƙanta su. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu.’ ”
Ku yi aure ku kuma haifi ’ya’ya maza da mata; ku nemi mata wa ’ya’yanku maza, ku kuma ba da ’ya’yanku mata ga aure, saboda su ma za su haifi ’ya’ya maza da mata. Ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu.