Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 29:21 - Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa game da Ahab ɗan Kolahiya da Zedekiya ɗan Ma’asehiya, waɗanda suke muku annabcin ƙarya da sunana. “Zan ba da su ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, zai kuwa kashe su a gaban idanunku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

21 “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce a kan Ahab ɗan Kolaya, da Zadakiya ɗan Ma'aseya, waɗanda suke yi muku annabcin ƙarya da sunana. Ga shi, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, zai kashe su a kan idonku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 29:21
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wahayin annabawanki ƙarya ne kuma marasa amfani; ba su tona zunubanki ba yadda za su iya ceto ki daga bauta ba. Sun yi miki annabcin ƙarya marar amfani.


Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya.


Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan maishe ka abin razana ga kanka da kuma ga dukan abokanka; da idanunka za ka gan takobin abokan gāba yana kashe su. Zan miƙa Yahuda duka ga sarkin Babilon, wanda zai kwashe su zuwa Babilon ya kuma kashe su da takobi.


Kai kuma Fashhur, da dukan waɗanda suke a gidanka za ku tafi zaman bauta a Babilon. A can za ku mutu a kuma binne ku, da kai da dukan abokanka waɗanda ka yi musu annabce-annabcen ƙarya.’ ”


Za ku iya ce, “Ubangiji ya tā da annabawa saboda mu a Babilon.”


A cikin annabawan Urushalima kuma na ga wani abin bantsoro. Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya. Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta, domin kada wani ya juya daga muguntarsa. Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni; mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ