Irmiya 27:22 - Sabon Rai Don Kowa 202022 ‘Za a kwashe su zuwa Babilon a can kuwa za su kasance sai ranar da na neme su,’ in ji Ubangiji. ‘Sa’an nan zan komo da su in maido da su wannan wuri.’ ” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki22 ‘Za a kwashe su a kai Babila, a can za su kasance har lokacin da zan sāke kulawa da su. Sa'an nan ne zan komo da su, in maishe su a wannan wuri.’ ” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.