Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 27:11 - Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Amma duk al’ummar da ta rusuna da wuyarta a ƙarƙashin karkiyar sarkin Babilon ta kuma bauta masa, zan bar al’ummar ta zauna a ƙasarta ta noma ta, ta kuma zauna a can, in ji Ubangiji.” ’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

11 Amma duk al'ummar da za ta ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyanta, ta kuma bauta masa, zan bar ta a ƙasarta, ta yi noman ƙasarta, ta zauna a ciki, ni Ubangiji na faɗa.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 27:11
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“ ‘ “Amma fa, duk al’umma ko mulkin da bai bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon ba bai kuwa rusunar da wuyarsa ga karkiyarsa ba, zan hukunta wannan al’umma da takobi, yunwa da annoba, in ji Ubangiji, har sai na hallaka ta ta wurin hannunsa.


Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka yi karkiyar itace da maɗaurai ka ɗaura a wuyanka.


Duk wanda ya zauna a wannan birni zai mutu ta takobi, yunwa ko annoba. Amma duk wanda ya fita ya miƙa kansa ga Babiloniyawa waɗanda suka kewaye ku zai rayu; zai kuɓutar da ransa.


“Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Duk wanda ya zauna a wannan birni zai mutu ta takobi, yunwa ko annoba, amma duk wanda ya je wurin Babiloniyawa zai rayu. Zai tsira da ransa, ya rayu.’


Na ba da wannan saƙo guda ga Zedekiya sarkin Yahuda. Na ce, “Ka rusunar da wuyanka a ƙarƙashin sarkin Babilon; ka bauta masa da kuma mutanensa, za ka kuwa rayu.


“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da na tattara mutanen Isra’ila daga al’ummai inda suke a warwatse, zan nuna kaina mai tsarki a cikinsu a idon al’ummai. Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu, wadda na ba wa bawana Yaƙub.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ