Game da Mowab. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Kaito ga Nebo, gama za tă lalace. Kiriyatayim za su kunyata a kuma kame ta; katagar za tă sha kunya ta kuma wargaje.
Masar, Yahuda, Edom, Ammon, Mowab da dukan waɗanda suke zaune a hamada a wurare masu nisa. Gama dukan waɗannan al’ummai marasa kaciya ne, har dukan gidan Isra’ila ma marasa kaciya ne a zuciya.”
Gidan Yaƙub zai zama kamar wuta, gidan Yusuf kuma kamar harshen wuta; gidan Isuwa zai zama kamar tattaka, za a kuma sa masa wuta yă ƙone. Babu wanda zai tsira daga gidan Isuwa.” Ni Ubangiji na faɗa.
Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Edom, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya fafari ɗan’uwansa da takobi, babu tausayi, domin ya ci gaba da fusata bai yarda yă huce daga fushinsa ba.
“Edom tana can, sarakunanta da dukan yerimanta; duk da ikonsu, sun kwanta tare da waɗanda aka kashe da takobi. Suna kwance tare da marasa kaciya, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.
Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda.
Game da Ammonawa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Isra’ila ba shi da ’ya’ya maza ne? Ba shi da magāda ne? To, me ya sa Molek ya mallaki Gad? Me ya sa mutanensa suka zama a garuruwansa?
Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Ammon, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu don kawai yă ƙwace ƙasar.
Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Mowab, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Gama ya ƙone ƙasusuwan sarkin Edom suka zama sai ka ce toka.