Irmiya 23:16 - Sabon Rai Don Kowa 202016 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Kada ku saurari abin da annabawan suke muku annabci; suna cika ku da sa zuciyar ƙarya. Suna maganar wahayi daga tunaninsu, ba daga bakin Ubangiji ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki16 Ubangiji Mai Runduna ya ce wa mazaunan Urushalima, “Kada ku kasa kunne ga maganar annabawa, Gama sukan cika kunnuwanku da ƙarairayi. Suna faɗar ganin damarsu, Ba faɗar Ubangiji ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.