Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 22:7 - Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Zan aika da mai hallakarwa a kanki, kowane mutum da makamansa, za su kuma yayyanka gumaguman al’ul na ki masu kyau su jefa su cikin wuta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

7 Zan shirya waɗanda za su hallaka ta. Kowannensu da makamansa, Za su sassare zaɓaɓɓun itatuwan al'ul ɗinta, a jefa su a wuta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 22:7
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta wurin jakadunka ka jibge zage-zage a kan Ubangiji. Ka kuma ce, ‘Da kekunan yaƙina masu yawa na hau ƙwanƙolin duwatsu, ƙwanƙolin mafi tsayi na Lebanon. Na sassare al’ul mafi tsayi fir mafi kyau. Na kai can wuri mafi nisa na kurminsa.


Zan hukunta ku gwargwadon ayyukanku, in ji Ubangiji. Zan sa wuta a kurminku da za tă cinye kome da yake kewaye da ku.’ ”


Sai sarkin ya yi fushi. Ya aiki mayaƙansa suka karkashe masu kisankan nan, aka kuma ƙone birninsu.


Buɗe ƙofofinki, ya Lebanon, don wuta ta cinye itatuwan al’ul naki.


Ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji, “Ina kawo al’umma daga nesa a kanku al’umma ce ta tun dā mai ƙarfin hali, mutane ne da ba ku san harshensu ba, waɗanda ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba.


Zan ƙara yawan gwaurayensu su fi yashin teku yawa. Da tsakar rana zan kawo mai hallakarwa a kan iyaye mata na samarinsu; farat ɗaya zan kawo musu wahala da razana.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ