Ku ji, ya ku mutane duka, ki saurara, ya ke duniya da dukan mazauna cikinki, bari Ubangiji Mai Iko Duka yă zama shaida a kanku, daga haikalinsa mai tsarki.
Ku zo kusa, ku al’ummai, ku kuwa saurara ku kasa kunne, ku mutane! Bari duniya ta ji, da kuma dukan abin da yake cikinta, duniya, da dukan abin da yake fitowa daga gare ta!
Yau, na kira sama da duniya, su zama shaidata a kanku. Idan kuka yi rashin biyayya, lalle za ku hallaka nan da nan daga ƙasar da kuke ƙetare Urdun ku gāda. Ba za ku daɗe a cikinta ba, amma za a kawar da ku ƙaƙaf.