Irmiya 21:9 - Sabon Rai Don Kowa 20209 Duk wanda ya zauna a wannan birni zai mutu ta takobi, yunwa ko annoba. Amma duk wanda ya fita ya miƙa kansa ga Babiloniyawa waɗanda suka kewaye ku zai rayu; zai kuɓutar da ransa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki9 Shi wanda ya zauna a birnin nan zai mutu da takobi, da yunwa, da annoba, amma shi wanda ya fita ya ba da kansa ga Kaldiyawa waɗanda suke kewaye da ku zai rayu ya tserar da ransa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan wannan, in ji Ubangiji, zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da kuma mutanen wannan birni waɗanda suka tsira daga annoba, takobi da kuma yunwa, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Zai kashe su da takobi; ba zai ji tausayinsu ko ya yi musu jinƙai ko ya yi juyayinsu ba.’