Irmiya 20:7 - Sabon Rai Don Kowa 20207 Ya Ubangiji, ka ruɗe ni, na kuwa ruɗu; ka fi ni ƙarfi, ka kuwa yi nasara. Na zama abin dariya dukan yini; kowa yana yi mini ba’a. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki7 “Ya Ubangiji ka ruɗe ni, na kuwa ruɗu, Ka fi ni ƙarfi, ka kuwa rinjaye ni. Na zama abin dariya dukan yini, Kowa yana ta yi mini ba'a. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Wata ƙungiyar Afikuriya da kuma masu bin ussan ilimin Sitoyik suka fara gardama da shi. Waɗansunsu suka ce, “Mene ne mai surutun nan yake ƙoƙarin faɗi?” Waɗansu suka ce, “Kamar yana wa’azin baƙin alloli ne.” Sun faɗa haka ne domin Bulus yana wa’azin labari mai daɗi game da Yesu da kuma tashin matattu.