Irmiya 2:7 - Sabon Rai Don Kowa 20207 Na kawo ku zuwa ƙasa mai albarka don ku ci amfaninta da abubuwa masu yalwar da take bayarwa. Amma kuka zo kuka ƙazantar da ƙasata kuka kuma mai da gādona abin ƙyama. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki7 Na kawo su zuwa ƙasa mai dausayi, Don su more ta su ci amfaninta, Amma da suka shiga, sun ƙazantar mini da ita, Suka sa ƙasar da na gādar musu ta zama abar ƙyama. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Suka kame birane masu katanga masu ƙarfi, da ƙasa masu ba da amfani; suka mallaki gidaje cike da kowane irin abu mai kyau, da rijiyoyin da aka riga aka haƙa, da gonakin inabi, da gonakin itatuwan zaitun da kuma itatuwan ba da ’ya’ya a yalwace a ciki. Suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba; suka ji daɗi cikin alherinka mai girma.