“Ka yi shelar wannan a Masar, ka kuma furta shi a Migdol; ka yi shelarsa kuma a Memfis da Tafanes. ‘Ku ɗauki matsayinku ku kuma shirya, gama takobi na cin waɗanda suke kewaye da ku.’
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Zan hallaka gumaka in kuma kawo ƙarshen siffofi a Memfis. Ba za a ƙara samun yerima a ƙasar Masar ba, zan kuma baza tsoro a duk fāɗin ƙasar.
Yă yi ta malala har zuwa cikin Yahuda, yă shafe ta, yana ratsa ta ciki har yă kai kafaɗa. Fikafikansa da ya buɗe za su rufe fāɗin ƙasarka, Ya Immanuwel!”
Fir’auna Neko ya sa shi a sarƙa a Ribla a ƙasar Hamat don kada yă yi mulki a Urushalima, sa’an nan ya sa wa Yahuda harajin talenti ɗari na azurfa, da talenti ɗaya na zinariya.
Na sani kana dogara da Masar, wadda take kamar karar masara, wadda in ka jingina a kai, za tă karye tă soki hannunka. Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga dukan wanda ya dogara da shi.
“A ƙarƙashin Heshbon masu gudun hijira suna tsaye ba mai taimako, gama wuta ta mutu daga Heshbon, harshen wuta daga tsakiyar Sihon; ta ƙone goshin Mowab, ƙoƙon kai na ’yan tayarwa masu surutu.
Ko da sun kuɓuta daga hallaka, Masar za tă tattara su, Memfis kuma za tă binne su. Sarƙaƙƙiya za tă mamaye kayan azurfansu, ƙayayyuwa su tsiro a cikin tentunansu.