Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 18:21 - Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Saboda haka ka kawo wa ’ya’yansu yunwa; ka miƙa su ga ikon takobi. Bari matansu su zama marasa ’ya’ya da gwauraye; bari a kashe mazansu, a kuma kashe samarinsu da takobi a yaƙi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

21 Saboda haka ka kawo wa 'ya'yansu yunwa, Ka bashe su ga takobi, Bari matansu su rasa 'ya'ya, mazansu su mutu, Ka sa annoba ta kashe mazansu, A kashe samarinsu da takobi a yaƙi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 18:21
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Na aiko muku annoba yadda na yi a Masar. Na karkashe samarinku da takobi, tare da kamammun dawakanku. Na cika hancinku da warin sansaninku, duk da haka ba ku juyo gare ni ba” in ji Ubangiji.


Mun zama marayu marasa ubanni, uwayenmu kamar gwauraye.


Zan ƙara yawan gwaurayensu su fi yashin teku yawa. Da tsakar rana zan kawo mai hallakarwa a kan iyaye mata na samarinsu; farat ɗaya zan kawo musu wahala da razana.


Mutuwa ta haura ta tagoginmu ta kuma shiga katangarmu; ta karkashe ’ya’ya a tituna ta kuma karkashe samari a dandali.


Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su, a cikin gidajensu kuma tsoro zai mamaye su. ’Yan maza da ’yan mata za su hallaka, haka ma jarirai da maza masu furfura.


Zan husata, in kuma kashe ku da takobi; matanku kuma, su ma su zama gwauraye, ’ya’yanku kuwa su zama marayu.


Alekzanda maƙerin ƙarafan nan ya yi mini mugunta ƙwarai. Ubangiji zai sāka masa saboda abin da ya yi.


Duk da haka ka san ni, ya Ubangiji; kana ganina ka kuma gwada tunanina game da kai. Ka ja su kamar tumakin da za a yanka! Ka ware su don ranar yanka!


Ya bashe su ga sarkin Babiloniyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a wuri mai tsarki, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka ga Nebukadnezzar.


Amma Sama’ila ya ce, “Yadda takobinka ya sa mata suka rasa ’ya’ya, haka mahaifiyarka za tă zama marar ’ya’ya a cikin mata.” Sama’ila kuwa ya kashe Agag a Gilgal a gaban Ubangiji.


Za a bayar da su ga takobi su kuma zama abincin karnukan jeji.


Saboda haka Ubangiji ba zai ji daɗin matasa ba, ba kuwa zai ji tausayin marayu da gwauraye ba, gama kowa marar sanin Allah ne da kuma mugu, kowane baki yana faɗin mugayen maganganu. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe.


Bakkunansu za su kashe samari; ba za su ji tausayin jarirai ba ba za su kuwa nuna jinƙai ga ’yan yara ba.


Mutanen da suke musu annabcin kuwa za a kore su zuwa titunan Urushalima saboda yunwa da kuma takobi. Babu wanda zai binne su, ko ya binne matansu, ko ’ya’yansu maza da mata. Zan aukar musu da masifar da ya dace da su.


Zan sheƙe ki da abin sheƙewa a ƙofofin birnin ƙasar. Zan kawo baƙin ciki da hallaka a kan mutanena, gama ba su canja hanyoyinsu ba.


Saboda haka, samarinta za su fāɗi a tituna; za a kawar da dukan sojojinta a wannan rana,” in ji Ubangiji.


“Ubangiji ya ƙi duk mayaƙan da suke tare da ni; ya sa wata runduna ta tayar mini ta kuma tattake samarina. Ubangiji ya tattake budurwa Diyar Yahuda kamar ’ya’yan inabi a wurin matsewa.


Zan hukunta ki da hukuncin matan da suke zina da kuma waɗanda suke zub da jini; zan kawo hakkin jini na fushina da kuma fushin kishina.


Akwai haɗin bakin sarakunanki a cikinki kamar rurin zaki mai yayyage ganimarsa; suna cin mutane, suna kwashe dukiya da abubuwa masu daraja suna mai da yawanci gwauraye a cikinki.


Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah; dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi, amma za a rufe bakunan maƙaryata.


Waɗanda suke jagorar wannan mutane suna ɓad da su, su ne waɗanda ake jagora aka sa suka kauce.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ