Ya Ubangiji, ƙarfina da katangana, mafakata a lokacin damuwa, gare ka al’ummai za su zo daga iyakokin duniya su ce, “Kakanninmu ba su mallaki kome ba sai allolin ƙarya, gumakan banza da ba su yi musu amfani ba.
Ya Ubangiji, sa zuciyar Isra’ila, duk waɗanda suka rabu da kai za su sha kunya. Waɗanda suka juya maka baya za a rubuta su a ƙura domin sun yashe Ubangiji, maɓulɓular ruwan rai.
Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona tsawa kuma daga Urushalima; duniya da sararin sama za su yi rawan jiki. Amma Ubangiji zai zama mafakar mutanensa, mafaka ga mutanensa Isra’ila.