Irmiya 17:11 - Sabon Rai Don Kowa 202011 Kamar makwarwar da ta kwanta a kan ƙwan da ba ita ta zuba ba haka yake da mutumin da ya sami arziki a hanyar da ba daidai ba. A tsakiyar rayuwarsa za su rabu da shi, a ƙarshe kuma zai zama wawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki11 “Kamar makwarwar da ta kwanta kan ƙwan da ba ita ta nasa ba, Haka yake ga wanda ya sami dukiyar haram, Yana gaɓar ƙarfinsa, za ta rabu da shi, A ƙarshe zai zama wawa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.