Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 12:12 - Sabon Rai Don Kowa 2020

12 A kan dukan tsaunukan nan na hamada masu hallakarwa za su zo, gama takobin Ubangiji zai ci daga wannan iyaka ƙasa zuwa wancan; ba wanda zai zauna lafiya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

12 A kan dukan tsaunukan nan na hamada Masu hallakarwa sun zo, Gama takobin Ubangiji yana ta kisa Daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, Ba mahalukin da yake da salama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 12:12
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ko da abokan gābansu sun kore su zuwa zaman bauta, a can zan umarci takobi yă kashe su. “Zan sa musu ido don mugunta ba don alheri ba.”


“Za ku yi kuka kuna cewa, ‘Wayyo, takobin Ubangiji sai yaushe za ka huta? Ka koma kubenka; ka huta, ka yi shiru.’


“Ko kuma in na kawo takobi a kan wannan ƙasa na kuma ce, ‘Bari takobin ya ratsa cikin dukan ƙasar,’ na kuma kashe mutanenta da dabbobinsu,


Takobin Ubangiji ya jiƙu da jini, ya rufu da kitse, jinin raguna da na awaki, kitse daga ƙodar raguna. Gama Ubangiji ya yi hadayar Bozra da kuma babban kisa a Edom.


Sai wani doki ya fito, ja wur. Aka ba wa mai hawansa iko yă ɗauke salama daga duniya yă kuma sa mutane su kashe juna. Aka ba shi babban takobi.


“Ku ma, ya Kushawa, za a kashe ku da takobina.”


Sa’ad da kwanakin ƙawanyarka sun ƙare, sai ka ƙone kashi ɗaya bisa uku na gashin da wuta a cikin birnin. Ka ɗauki kashi ɗaya bisa uku ka yayyanka shi da takobi kewaye da birnin. Ka kuma watsar da kashi ɗaya bisa uku a iska. Gama zan fafare su da takobin da aka zāre.


Ba za a ƙara yabi Mowab ba; a Heshbon mutane za su shirya mata maƙarƙashiya. ‘Zo, mu tafi mu kawo ƙarshe ga wannan al’umma.’ Ke kuma, ya Madmen za ki yi shiru; takobi zai fafare ki.


“Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, kun yi mini rashin biyayya; ba ku yi shelar ’yanci don ’yan’uwanku ba. Saboda haka yanzu na yi muku shelar ’yanci in ji Ubangiji, ’yanci ga mutuwa ta takobi, annoba da kuma yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga sauran mulkokin duniya.


In kuma suka tambaye ka, ‘Ina za mu tafi?’ Sai ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Waɗanda aka ƙaddara ga mutuwa, ga mutuwa za su; waɗanda aka ƙaddara ga takobi, ga takobi za su; waɗanda aka ƙaddara ga yunwa, ga yunwa za su; waɗanda aka ƙaddara ga zaman bauta, ga zaman bauta za su.’


“Ta da idanu ki duba tsaunuka ki gani. Akwai wani wurin da ba a kwana da ke ba? A gefen hanya kin zauna kina jiran masoyanki, kin zauna kamar makiyayi a hamada. Kin ƙazantar da ƙasar da karuwancinki da muguntarki.


“Babu salama ga mugaye,” in ji Allahna.


Zan watsar da ku cikin al’ummai, in kuma ja takobina in kore ku. Ƙasarku za tă zama kufai, biranenku kuma su zama kango.


Zan sa kibiyoyina su bugu da jini, yayinda takobina yana cin nama, jinin kisassu da na kamammu, kawunan shugabannin abokan gāba.”


An ji kuka a filayen tuddai, kuka da roƙon mutanen Isra’ila, domin sun lalace hanyoyinsu sun kuma manta da Ubangiji Allahnsu.


Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Dukan ƙasar za tă zama kufai, ko da yake ba zan hallaka ta gaba ɗaya ba.


Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada ka shiga gidan da akwai abincin makoki; kada ka tafi ka yi makoki ko ka nuna juyayi, domin na janye albarkata, ƙaunata da tausayina daga wannan mutane,” in ji Ubangiji.


Dukan wannan ƙasa za tă zama kango, kuma waɗannan al’ummai za su bauta wa sarkin Babilon shekaru saba’in.


“Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Ana jin kukan tsoro, razana, ba salama ba.


Amma wannan rana ta Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki ranar ɗaukar fansa, gama ɗaukar fansa a kan maƙiyansa. Takobi zai yi ta ci sai ya gamsu, sai ya kashe ƙishirwansa da jini. Gama Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, zai miƙa hadaya a ƙasar arewa kusa da Kogin Yuferites.


An hana ni salama; na manta da ko mene ne ake kira wadata.


Domin zan karkashe adalai da kuma mugaye, ba zan rufe takobina a kan kowa daga kudu zuwa arewa ba.


“Kai kuma, ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da Ammonawa da kuma zarginsu. “ ‘Takobi, takobi, an ja don kisa, an goge don cinyewa yana haske kamar walƙiya!


Mun sa zuciya ga salama amma ba lafiya, mun sa zuciya ga lokacin warkarwa amma sai ga razana.


“Ɗan mutum, yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “ ‘Takobi, takobi, wasasshe da kuma gogagge,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ