“Ina amfanin gunki da mutum ne ya sassaƙa? Ko siffar da take koyar da ƙarya? Gama wanda ya yi shi yana dogara ne ga halittarsa; ya yi gumakan da ba sa magana.
Ba wanda yakan dakata ya yi tunani, ba wanda yake da sani ko fahimi ya ce, “Da rabinsa na yi amfani da shi don hura wuta; na ma gasa burodi a kan garwashinsa, na gasa nama na kuma ci. Ya kamata in yi abin ƙyama daga abin da ya rage? Ya kamata in rusuna wa guntun katako?”
“Mutanena wawaye ne; ba su san ni ba. Su ’ya’ya ne marasa azanci; ba su da fahimi. Suna da dabarar aikata mugunta; ba su san yadda za su aikata alheri ba.”
Kuna ce wa itace, ‘Kai ne mahaifina,’ ga dutse kuma, ‘Kai ne ka haife ni.’ Sun juye mini bayansu ba fuskokinsu ba; duk da haka sa’ad da suna cikin wahala, sukan ce, ‘Zo ka cece mu!’