Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 7:11 - Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Ko da yake Dokar Musa ta ce dole firistoci su kasance zuriyar Lawi, waɗannan firistoci ba su iya sa wani yă zama cikakke ba. Saboda akwai bukata wani firist kamar Melkizedek ya zo, a maimakon wani daga iyalin Haruna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

11 Gama da a ce kammala tana samuwa ta wurin firistoci na zuriyar Lawi (don ta gare su ne jama'a suka karɓi shari'a), wace bukata kuma ake da ita ta wani firist dabam ya bayyana kwatancin ɗabi'ar Malkisadik, wanda za a ambata ba kwatancin ɗabi'ar Haruna ba?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 7:11
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama da a ce alkawari na fari ba shi da wani laifi, da ba sai an sāke neman wani ba.


Ba na ajiyar alherin Allah a gefe, gama da a ce ana samun adalci ta wurin Doka, ai, da Kiristi ya mutu a banza ke nan!”


shi wannan ya zama firist ta wurin rantsuwar da Allah ya yi da ya ce masa, “Ubangiji ya rantse, ba kuwa zai canja zuciyarsa ba, ‘Kai firist ne na har abada.’ ”


Canjin nan a Dokar Allah ya ƙara fitowa fili da wani firist dabam wanda yake kamar Melkizedek ya bayyana.


Ya kuma ya ce a wani wuri, “Kai firist ne na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”


Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma a ce Allah ya san ku, yaya kuke sāke komawa ga ƙa’idodin duniya marasa ƙarfi, abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu ne?


inda Yesu, wanda ya sha gabanmu, ya shiga a madadinmu. Ya zama babban firist na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.


Allah kuwa ya naɗa shi yă zama babban firist, bisa ga tsarin Melkizedek.


Haka yake, sa’ad da muke ’yan yara, mun kasance cikin bauta a ƙarƙashin ƙa’idodin duniya.


wannan ya kasance haka domin an haifi Lawi daga baya a iyalin Ibrahim wanda ya ba wa Melkizedek kashi ɗaya bisa goma.


Gama in aka canja yadda ake zaɓan firist, dole a canja Dokar ita ma.


Mutumin da muke wannan zance a kai, ai, shi na wata kabila ce dabam, wadda ba wani daga kabilar da ya taɓa yin hidima a bagade.


Sa’ad da aka shirya kome haka, sai firistoci suka shiga kullum cikin ɗaki na waje don su yi hidimarsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ