Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 6:7 - Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ƙasar da take shan ruwan sama da yake fāɗi a kanta kullum da kuma take ba da hatsin da yake da amfani ga waɗanda ake noma dominsu, takan sami albarkar Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

7 Ƙasa ma da take shanye ruwan da ake yi mata a kai a kai, take kuma fid da tsire-tsire masu amfani ga waɗanda ake noma ta dominsu, Allah yakan sa mata albarka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 6:7
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku shuka wa kanku adalci, ku girbe ’ya’yan jinƙai marar ƙarewa, ku kuma nome ƙasar da ba a nome ba; gama lokaci ne na neman Ubangiji, sai ya zo ya zubo adalci a kanku.


Gama zan zuba ruwa a ƙeƙasasshiyar ƙasa, rafuffuka kuma a busasshiyar ƙasa; zan ba da Ruhuna ga ’ya’yanka, albarkata kuma ga zuriyarka.


Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna.


Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka.


Zan albarkace su in kuma sa tuduna kewaye da su. Zan zubo yayyafi a lokacinsa; za a kasance da yayyafin albarka.


Zai sami albarka daga Ubangiji da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.


Zan aika muku da irin albarka a shekara ta shida har da ƙasar za tă ba da amfani isashe na shekara uku.


Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.


Saboda haka ya je gunsa ya sumbace shi. Sa’ad da Ishaku ya ji ƙanshin rigunansa, sai ya sa masa albarka ya ce, “Aha, ƙanshin ɗana yana kama da ƙanshin jejin da Ubangiji ya sa wa albarka ne.


Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance.


Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.


Manomi mai aiki sosai ya kamata yă zama na fari wajen samun rabon amfanin gona.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ