Ibraniyawa 4:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Maganar Allah tana da rai, tana kuma da ƙarfin aiki. Ta fi kowane takobi mai baki biyu kaifi. Maganarsa takan ratsa har ciki-ciki, tana raba rai da ruhu, gaɓoɓi da kuma ɓargon ƙashi; har sai ta tone ainihi wane ne muke. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki12 Domin Maganar Allah rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki, ta fi kowane irin takobi kaifi, har tana ratsa rai da ruhu, da kuma gaɓoɓi, har ya zuwa cikin ɓargo, tana kuma iya rarrabe tunanin zuciya da manufarta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.