Ibraniyawa 13:4 - Sabon Rai Don Kowa 20204 Aure yă zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki4 Kowa yă girmama aure, Gădon aure kuwa yă zauna marar dauɗa, don fasikai da mazinata Allah zai hukunta su, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.