Duk wanda ya ce, “Ina ƙaunar Allah,” amma yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne. Gama duk wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba.
Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa ’yan’uwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya.
Dole kullum mu gode wa Allah saboda ku, ’yan’uwa, haka kuwa ya dace, domin bangaskiyarku tana girma gaba-gaba, ƙaunar da kowannenku yake yi wa juna kuwa tana ƙaruwa.
Ku ’yan’uwana, an kira ku ga zama ’yantattu. Amma kada ku yi amfani da ’yancinku don aikata ayyukan mutuntaka a maimakon haka, ku yi hidimar juna da ƙauna.
Gama a cikin Kiristi Yesu, kaciya ko rashin kaciya ba su da wani amfani. Abin da kawai yake da amfani shi ne, bangaskiyar da take bayyana kanta ta wurin ƙauna.