Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 11:3 - Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Ta wurin bangaskiya ne muka fahimci cewa an halicci duniya bisa ga umarnin Allah, saboda an halicce abin da ake gani daga abin da ba a gani.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

3 Ta wurin bangaskiya muka fahimta, cewa ta faɗar Allah ce aka tsara duniya, har ma abubuwan da ake gani, daga abubuwan da ba a gani ne, suka kasance.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 11:3
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai, rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa.


Amma da gangan suke manta cewa tun dā can ta wurin maganar Allah sammai suka kasance aka kuma yi ƙasa daga ruwa ta wurin ruwa kuma.


Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi.


Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na mai da kai uban al’ummai masu yawa.” Shi ubanmu ne a gaban Allah, wanda a cikinsa ya gaskata, Allahn da yake ba da rai ga matattu, yake kuma kiran abubuwan da ba su kasance ba su zama kamar sun kasance.


“Allahn da ya halicci duniya da kome da yake cikinta shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da aka gina da hannuwa.


“Ya Ubangijinmu da Allahnmu, ka cancanci ɗaukaka da girma da iko, domin ka halicci dukan abubuwa, kuma ta wurin nufinka aka halicce su suka kuma kasance.”


amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya.


“Ka faɗa musu wannan, ‘Waɗannan alloli, waɗanda ba su yi sammai da ƙasa ba, za su hallaka daga duniya da kuma daga ƙarƙashin sammai.’ ”


A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa.


Ku ɗaga idanunku ku duba sammai. Wane ne ya halicce dukan waɗannan? Wane ne ya fitar da rundunar taurari ɗaya-ɗaya, yana kiransu, kowanne da sunansa. Saboda ikonsa mai girma da kuma ƙarfinsa mai girma, babu ko ɗayansu da ya ɓace.


“Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai, ’yan adam ne kamar ku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu.


Shi da yake Rabon Yaƙub ba kamar waɗannan yake ba, gama shi ne Mahaliccin abubuwa duka, har da Isra’ila, kabilar gādonsa Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.


Gama ya yi magana, abu ya kuwa kasance; ya umarta, ya kuwa tsaya daram.


A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai.


domin an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da kuma addu’a.


waɗanda suka ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikokin zamani mai zuwa,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ