Ku daga idanunku zuwa sammai ku dubi duniya a ƙasa; sammai za su ɓace kamar hayaƙi, duniya za tă shuɗe kamar riga mazaunanta kuma su mutu kamar ƙudaje. Amma cetona zai dawwama har abada, adalcina ba zai taɓa kāsa ba.
Za a tumɓuke dukan taurarin sammai za a kuma nannaɗe sararin sama kamar littafi; dukan rundunar sama za su fāffāɗi kamar ganyayen da suka yanƙwane daga kuringa, kamar ’ya’yan ɓauren da suka bushe daga itacen ɓaure.
“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Simirna, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomin wannan da yake na Farko da na Ƙarshe, wanda ya mutu ya kuma sāke tashi da rai.
wadda ta ce, “Rubuta a cikin naɗaɗɗen littafi abin da ka gani ka kuma aika ta zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai, zuwa Afisa, Simirna, Fergamum, Tiyatira, Sardis, Filadelfiya, da kuma Lawodiseya.”
Wane ne ya taɓa yin haka ya kuma sa ya faru, yana kira ga tsararraki daga farko? Ni, Ubangiji ina can tun farkonsu ni kuma ina can har ƙarshe, Ni ne shi.”