Hosiya 9:4 - Sabon Rai Don Kowa 20204 Ba za su zuba hadayun ruwan inabi ga Ubangiji ba, ba kuwa hadayunsu za su gamshe shi ba. Irin hadayun nan za su zama musu kamar burodin masu makoki; duk wanda ya ci su zai ƙazantu. Wannan abincin zai zama na kansu ne; ba zai zo cikin haikalin Ubangiji ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki4 Ba za su yi wa Ubangiji hadaya ta sha ba. Ba za su faranta zuciyarsa da sadakoki ba. Abincinsu zai zama irin na masu makoki. Duk wanda ya ci shi zai haramta. Gama abincinsu zai yi musu maganin yunwa ne kawai, Ba za su kai shi Haikalin Ubangiji ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Amma duk ya miƙa hadayar bijimi yana kama da wanda ya kashe mutum, kuma duk wanda ya miƙa ɗan rago, kamar wanda ya karye wuyan kare; duk wanda ya miƙa hadaya ta gari yana kama da wanda ya yi sadakar jinin alade, kuma duk wanda ya ƙone turaren tuni, kamar wanda yake bauta gunki ne. Sun zaɓi hanyoyinsu, rayukansu kuma suna jin daɗin abubuwan banƙyamarsu;