“Saboda dukan muguntarsu a Gilgal, na ƙi su a can. Saboda ayyukansu na zunubi, zan kore su daga gidana. Ba zan ƙara ƙaunace su ba; dukan shugabanninsu ’yan tawaye ne.
Kaiton waɗanda suke zuwa manyan zurfafa don su ɓoye shirye-shiryensu daga Ubangiji, waɗanda suke aikinsu cikin duhu su yi tunani, “Wa yake ganinmu? Wa zai sani?”
Suka ce, “Zo mu shirya wa Irmiya maƙarƙashiya; gama koyarwar doka da firist ya yi ba za tă ɓace ba, haka ma shawara daga mai hikima da kuma magana daga annabawa. Saboda haka ku zo, mu fāɗa masa da harsunanmu kada mu saurari wani abin da zai faɗa.”
Ya Ubangiji, idanunka ba sa ganin gaskiya? Ka buge su, amma ba su ji zafi ba; ka ragargaza su, amma suka ƙi su gyara. Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse suka ƙi su tuba.