Hosiya 2:7 - Sabon Rai Don Kowa 20207 Za tă bi kwartayenta amma ba za tă kama su ba; za tă neme su amma ba za tă same su ba. Sa’an nan za tă ce, ‘Zan koma ga mijina na fari, gama dā ya fi mini yadda nake a yanzu.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki7 Za ta bi samarinta, amma ba za ta tarar da su ba. Za ta neme su, amma ba za ta same su ba. Sa'an nan za ta ce, ‘Zan koma wurin mijina na fari, Gama zamana na dā ya fi na yanzu!’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Aka kore shi daga cikin mutane aka kuma ba shi tunani irin na dabba; ya yi zama tare da jakunan jeji, ya kuma ci ciyawa kamar shanu; jikinsa kuma ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.
Lalle za mu aikata duk abin da muka ce za mu yi. Za mu ƙone turare ga Sarauniyar Sama za mu kuma miƙa hadayun sha gare ta kamar dai yadda mu da kakanninmu, sarakunanmu da fadawanmu muka yi a garuruwan Yahuda da kuma kan titunan Urushalima. A lokacin muna da abinci a yalwace muna kuma da arziki ba mu kuma da wata damuwa.