Muguntarka za tă hukunta ka; jan bayanka zai tsawata maka. Sai ka lura ka kuma gane yaya mugu da kuma ɗaci suke a gare ka sa’ad da ka rabu da Ubangiji Allahnka kuma ba ka tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
Kai mai albarka ne, ya Isra’ila! Wane ne yake kamar ka, mutanen da Ubangiji ya ceta? Shi ne mafakarka da mai taimakonka da kuma takobinka mai ɗaukaka. Abokan gābanka za su zo neman jinƙai a gabanka, za ka kuwa tattake masujadansu.”
Kun kuma ce, ‘Mun gaji da irin wannan wahala!’ Kuna hura mini hancin reni,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Sa’ad da kuka kawo raunannu, gurguntattun dabbobi, ko kuma dabbobi masu fama da cuta, kuka kuma miƙa su hadaya, kuna gani zan karɓi wannan daga gare ku?” In ji Ubangiji.
Ya miƙa hadayu ga allolin Damaskus, waɗanda suka ci shi a yaƙi; gama ya yi tunani, “Da yake allolin sarakunan Aram sun taimake su, zan miƙa hadayu domin su taimake ni.” Amma suka zama sanadin fāɗuwarsa da kuma fāɗuwar dukan Isra’ila.