Saboda haka zaki daga kurmi zai fāɗa musu, kyarkeci kuma daga hamada zai cinye su, damisa za tă yi musu ƙawanya kusa da garuruwansu yă yayyage duk wanda ya kuskura ya fita, gama tawayensu da girma yake jan bayansu kuma yana da yawa.
Dabbar da na gani ta yi kamar damisa, amma tana da ƙafafu kamar na beyar, bakinta kuma ya yi kamar na zaki. Macijin nan ya ba wa dabbar ƙarfinsa da gadon sarautarsa da kuma ikonsa mai girma.