12 An yi ajiyar laifin Efraim, aka lissafta zunubansa.
12 “An ƙunshe muguntar Ifraimu, Zunubinsa kuwa an ajiye shi a rumbu.
Za a daure laifofina a cikin jaka; za ka rufe zunubaina.
Amma saboda taurinkanka da zuciyarka marar tuba, kana tara wa kanka fushi a ranar fushin Allah, sa’ad da za a bayyana hukuncinsa mai adalci.
An ce ‘Allah yana tara wa ’ya’yan mutum horon da zai ba mutumin.’ Bari yă ba mutumin horo don yă san ya yi haka!
Ko da yake ka wanke kanka da sabulu ka yi amfani da sabulu mai yawa, duk da haka har yanzu tabon laifinka yana nan a gabana,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.