A maimakon tagulla zan kawo zinariya, azurfa kuma a maimakon baƙin ƙarfe. A maimakon katako zan kawo tagulla, baƙin ƙarfe kuma a maimakon duwatsu. Zan sa salama ta zama gwamnarki adalci kuma mai mulkinki.
“Darajar Lebanon za tă zo wurinki, itatuwan fir da dai ire-irensu da kuma itatuwan saifires duka za su zo don su ƙayatar da wurina mai tsarki; zan kuma ɗaukaka wurin ƙafafuna.