Habakkuk 2:19 - Sabon Rai Don Kowa 202019 Kaito wanda ya ce da katako, ‘Rayu!’ Ko kuwa dutse marar rai, ‘Farka!’ Zai iya bishewa ne? An dalaye shi da zinariya da azurfa; ba numfashi a cikinsa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki19 Tasa ta ƙare, shi wanda ya ce da abin da aka yi da itace, ‘Farka!’ Ya kuma ce wa dutse wanda ba ya ji, ‘Tashi!’ Wannan zai iya koyarwa? Ga shi, an dalaye shi da zinariya da azurfa, Ba ya numfashi ko kaɗan. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.