Habakkuk 1:16 - Sabon Rai Don Kowa 202016 Saboda haka yakan yi hadaya wa abin kamun kifinsa yă kuma ƙona turare wa ragarsa, domin ta wurin abin kamun kifinsa ne yake yin rayuwar jin daɗi yă kuma zaɓi irin abincin da yake so. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki16 Domin haka sukan miƙa hadaya ga tarunsa, Su ƙona turare ga ragarsu, Domin su ne suka jawo musu wadata, da abinci mai yawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.
Lalle za mu aikata duk abin da muka ce za mu yi. Za mu ƙone turare ga Sarauniyar Sama za mu kuma miƙa hadayun sha gare ta kamar dai yadda mu da kakanninmu, sarakunanmu da fadawanmu muka yi a garuruwan Yahuda da kuma kan titunan Urushalima. A lokacin muna da abinci a yalwace muna kuma da arziki ba mu kuma da wata damuwa.