Habakkuk 1:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Ya Ubangiji, ba tun fil azal kake ba? Ya Allahna, Mai Tsarkina, ba za mu mutu ba. Ya Ubangiji ka sanya su su tabbatar da hukunci; Ya Dutse, ka naɗa su don su yi hukunci. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki12 Ba kai ne madawwami ba? Ya Ubangiji Allahna Mai Tsarki. Ba za mu mutu ba. Ya Ubangiji, kai ne ka sa su su yi hukunci, Ya dutse, kai ne ka kafa su don su yi horo. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansa da kuma Mai Tsarkin nan na Isra’ila gare shi wanda al’ummai suka rena suka kuma ki, ga bawan masu mulki. “Sarakuna za su gan ka su kuma miƙe tsaye, sarakuna za su gani su kuma rusuna, saboda Ubangiji, wanda yake mai aminci, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, wanda ya zaɓe ka.”
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.