Gayus, mai masauƙina, mai kuma saukar da dukan ’yan Ikkilisiya, yana gaishe ku. Erastus, mai bi da ayyukan jama’ar gari, da kuma ɗan’uwanmu Kwartus, suna gaishe ku.
Ina so ku sani ’yan’uwa cewa na yi shirin zuwa wurinku sau da dama (amma aka hana ni yin haka sai yanzu). Na so in zo domin in sami mutane wa Kiristi a cikinku, kamar yadda na yi a cikin sauran Al’ummai.
’Yan’uwa, bari in yi muku misali da rayuwarmu ta yau da kullum. Kamar dai yadda ba mai kawarwa ko yă ƙara wani abu cikin alkawarin da mutane suka kafa, haka yake a wannan batu.
’Yan’uwa, in an kama wani yana cikin yin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ku lura da kanku, domin kada maimakon dawowa da ɗan’uwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba.