Saboda wannan, sa’ad da ban iya jimrewa ba, sai na aika domin in sami labarin bangaskiyarku, da fata kada yă zama mai jarraban nan ya riga ya jarrabce ku, ƙoƙarinmu kuma yă zama banza.
Na tafi ne bisa ga wani wahayi. Da na kai can, sai na bayyana musu bisharar da nake wa’azi a cikin Al’ummai. Na yi haka a keɓance a gaban waɗanda suke shugabanni, don tsoro kada gudun da nake yi, ko kuwa na riga na yi, yă zama a banza.
Saboda haka, ƙaunatattu ’yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yă jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.
Amma na ce, “Na yi aiki a banza; na kashe duk ƙarfina a banza da wofi. Duk da haka abin da yake nawa yana a hannun Ubangiji, ladana kuma tana a wurin Allahna.”