Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă ’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko.
Amma hidimar da Yesu ya karɓa tana da fifiko a kan tasu, kamar yadda alkawarin da shi ne yake matsakanci ya fi na dā fifiko nesa, an kuma kafa shi a kan alkawura mafi kyau.
Yana da rashin jituwa da mutanen Taya da na Sidon; sai suka haɗa kai suka nemi ganawa da shi. Bayan suka sami goyon bayan Bilastus, amintaccen bawan sarki, sai suka nemi salama, domin sun dogara ga ƙasar sarkin don samun abincinsu.