Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Galatiyawa 3:18 - Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Gama da a ce gādon yă dangana a kan doka ne, ai, da ba zai dangana a kan alkawari ba; amma Allah cikin alherinsa ya ba wa Ibrahim gādon ta wurin alkawari.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

18 Don da gādon nan ta hanyar Shari'a yake samuwa, ashe, da ba zai zama na alkawarin ke nan ba. Amma Allah ya bai wa Ibrahim ta wurin alkawari ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Galatiyawa 3:18
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba na ajiyar alherin Allah a gefe, gama da a ce ana samun adalci ta wurin Doka, ai, da Kiristi ya mutu a banza ke nan!”


Ya tuna da alkawarinsa mai tsarki da ya ba wa bawansa Ibrahim.


In kuwa ku na Kiristi ne, to, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda kuma bisa ga alkawarin nan.


In kuwa mu ’ya’ya ne, to, mu magāda ne, magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.


Dukanku ’ya’yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu.


Alkawaran nan fa ga Ibrahim ne aka faɗa da kuma wani zuriyarsa. Nassi bai ce, “da zuriyoyi ba” wanda ya nuna kamar mutane da yawa, amma “ga zuriyarka,” wanda yake nufin mutum ɗaya, wanda shi ne Kiristi.


Doka ba tă dangana ga bangaskiya ba; a maimakon haka, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”


Dukan waɗanda suka dogara ga kiyaye Doka la’anannu ne, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda bai ci gaba da yi dukan abubuwan da aka rubuta a Littafin Doka ba.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ