A wani lokaci can baya mu ma wawaye ne, marasa biyayya, aka ruɗe mu, sha’awace-sha’awace da kwaɗayi iri-iri suka daure mu, muka yi zaman ƙiyayya da kishi, aka ƙi mu, mu kuma muka ƙi juna.
Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah.
Saboda haka, alkawari yakan zo ta wurin bangaskiya ne, domin yă zama ta wurin alheri, don a tabbatar wa dukan zuriyar Ibrahim ba kawai ga waɗanda suke na doka ba amma har ma ga waɗanda suke na bangaskiyar Ibrahim. Shi ne kuwa mahaifinmu duka.
“In kuwa ya zama muna so mu sami zaman marasa laifi a gaban Allah ta wurin dogara ga Kiristi, sa’an nan an same mu mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, ko wannan zai nuna Kiristi yana ƙarfafa zunubi ke nan? A’a, ko kusa!