Fitowa 8:3 - Sabon Rai Don Kowa 20203 Nilu zai cika da kwaɗi. Za su haura zuwa cikin fadanka da kan gadonka, cikin gidajen bayinka da kan mutanenka, cikin kwanonin toye-toyenka da na cin abincinka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki3 Nilu zai cika da kwaɗi, za su tashi, su shiga cikin fādarka, da ɗakin kwanciyarka, da gadonka, har da gidajen fadawanka da jama'arka. Za su kuma shiga matuyanka da kwanon tuwonka, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Amma Yehosheba, ’yar Sarki Yehoram, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya ta sace shi daga cikin ’ya’yan gidan sarauta waɗanda ake shiri a kashe, ta sa shi tare da mai renonsa a ɗakin kwana. Haka fa, Yehosheba ’yar sarki Yoram, matar Yehohiyada firist, ta yi, gama ita ’yar’uwar Ahaziya ce, ta ɓoye Yowash don kada Ataliya tă kashe shi.