Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 8:20 - Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tashi da sassafe ka sadu da Fir’auna a lokacin da za shi kogi, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, bari mutanena su tafi, don su yi mini sujada.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

20 Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe ka sami Fir'auna a daidai lokacin da ya fita za shi rafi, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 8:20
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka je wurin Fir’auna da safe, yayinda za shi kogi. Ka jira a bakin Nilu don ka sadu da shi, ka ɗauki sandan nan da ya canja zuwa maciji a hannunka.


Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe, ka sadu da Fir’auna, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, Ka bar mutanena su tafi don su yi mini sujada,


Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka je wurin Fir’auna, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada.


“Dattawan Isra’ila za su saurare ka. Sa’an nan da kai da dattawan Isra’ila, za ku tafi wurin sarkin Masar, ku ce masa, ‘Ubangiji, Allah na Ibraniyawa, ya sadu da mu. Bari mu yi tafiyar kwana uku zuwa cikin hamada domin mu yi hadaya wa Ubangiji Allahnmu.’


Sai ’yar Fir’auna ta gangara zuwa kogi domin tă yi wanka, bayinta kuwa suna tafiya a bakin kogi. Sai ta ga kwandon a ciyawa, ta aiki ɗaya daga cikin masu hidimarta tă ɗauko mata.


na gaya maka, “Ka bar ɗana yă tafi domin yă yi mini sujada.” Amma ka ƙi ka bari yă tafi, saboda haka zan kashe ɗan farinka.’ ”


Daga bisani sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Bari mutanena su tafi domin su yi mini biki a hamada.’ ”


Sai suka ce, “Allah na Ibraniyawa ya sadu da mu. Yanzu bari mu ɗauki tafiyar kwana uku cikin hamada domin mu miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnmu, don kada yă buga mu da annoba ko takobi.”


In ba ka bar mutanena suka tafi ba, zan turo da tarin ƙuda a kanka da bayinka, a kan mutanenka da cikin gidajenka. Gidajen Masarawa za su cika da ƙudaje, har ma da ƙasa inda za su taka.


Ya aika da tarin ƙudajen da suka cinye su, da kwaɗin da suka wahalshe su.


Ya yi magana, sai tarin ƙudaje suka fito, cinnaku kuma ko’ina a ƙasar.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ