Fitowa 6:6 - Sabon Rai Don Kowa 20206 “Saboda haka, ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ni ne Ubangiji, zan kuma fitar da ku daga bauta ta Masarawa. Zan ’yantar da ku daga zama bayinsu, da ƙarfina zan fanshe ku, in kawo hukunci mai zafi a kansu, don in cece ku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki6 Sai ka faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ni Ubangiji zan 'yantar da ku daga wulakancin nan da Masarawa suke yi muku. Zan kuɓutar da ku daga bautar Masarawa. Da ƙarfi zan aikata hukuntaina masu iko don in cece ku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Akwai wani allahn da ya taɓa yin ƙoƙari yă ɗauko wa kansa wata al’umma daga wata al’umma, ta wurin gwaje-gwaje, ta wurin alamu masu banmamaki da al’ajabai, ta wurin yaƙi, ta wurin hannu mai iko, da kuma hannu mai ƙarfi, ko kuwa ta wurin ayyuka masu bangirma da na banmamaki, kamar dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi saboda ku a Masar, a kan idanunku?