Fitowa 6:1 - Sabon Rai Don Kowa 20201 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu za ka gan abin da zan yi da Fir’auna. Zan sa shi dole yă bar su su tafi, har ma yă iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki1 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Yanzun nan, za ka ga abin da zan yi da Fir'auna. Gama zan tilasta shi ya bar su su fita, har ma ya iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Akwai wani allahn da ya taɓa yin ƙoƙari yă ɗauko wa kansa wata al’umma daga wata al’umma, ta wurin gwaje-gwaje, ta wurin alamu masu banmamaki da al’ajabai, ta wurin yaƙi, ta wurin hannu mai iko, da kuma hannu mai ƙarfi, ko kuwa ta wurin ayyuka masu bangirma da na banmamaki, kamar dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi saboda ku a Masar, a kan idanunku?