Fitowa 3:17 - Sabon Rai Don Kowa 202017 Na kuma yi alkawari, zan fitar da ku daga azabarku a Masar zuwa ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasa mai zub da madara da zuma.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki17 Ya yi alkawari cewa zai fisshe ku daga wahalar Masar zuwa ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. Ƙasa wadda take mai ba da yalwar abinci.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Isra’ilawa sun yi tafiya a jeji shekaru arba’in, har sai da dukan mazan da suka kai shekarun shiga soja da suka bar Masar suka mutu, domin ba su yi wa Ubangiji biyayya ba. Gama Ubangiji ya rantse cewa ba zai bar su su ga ƙasar da ya yi wa iyayensu alkawari da rantsuwa cewa zai ba su ba, ƙasar da zuma da madara suke kwarara, ƙasar da take cike da albarka.