Amma mai mulkin majami’ar ya ji haushi da Yesu ya yi warkarwa a ranar Asabbaci. Sai ya ce wa mutanen, “Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Saboda haka, ku zo a ranakun nan a warkar da ku, ba ranar Asabbaci ba.”
“Kwana shida za ku yi aikinku, amma a rana ta bakwai, kada ku yi aiki, saboda saniyarku da jakinku su huta, haka kuma bawan da aka haifa a gidanku, da kuma baƙon da yake a cikinku yă wartsake.
“ ‘Akwai kwanaki shida da za ku iya yin aiki, amma rana ta bakwai, Asabbaci ne na hutu, rana mai tsarki ga jama’a. Kada ku yi wani aiki a ko’ina kuke da zama, Asabbaci ne ga Ubangiji.
Kwana shida za ku yi aiki, amma rana ta bakwai za tă zama rana mai tsarki, Asabbaci ne na hutu ga Ubangiji. Duk wanda ya yi aiki a wannan rana dole a kashe shi.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a rufe ƙofa ta fili na can cikin da take fuskantar gabas ranaku shida na aiki, amma a ranar Asabbaci da kuma a ranar ganin Sabuwar Wata a buɗe ta.