Waɗannan su ne dokokin da Ubangiji ya furta da babbar murya ga taronku gaba ɗaya, a can dutse ta tsakiyar wuta, girgije da kuma baƙin duhu; bai kuma ƙara kome ba. Sa’an nan ya rubuta su a kan alluna biyu na dutse, ya kuma ba ni su.
Ya kasance a cikin taron nan a hamada, tare da mala’ikan da ya yi magana da shi a Dutsen Sinai, da kuma tare da kakanninmu; ya kuma karɓi kalmomi masu rai don yă miƙa mana.
Ubangiji kuwa ya sāke yin rubutu a waɗannan alluna abin da ya rubuta a allunan farko, wato, Dokoki Goma da ya furta a kan dutse a tsakiyar wuta, a ranar da mutane suka taru. Sai Ubangiji ya ba ni su.
“Ka sauko a kan Dutsen Sinai; ka yi musu magana daga sama. Ka ba su ƙa’idodi da dokokin da suke masu adalci da kuma daidai, ka ba su farillai da umarnai da suke da kyau.