“Ku yi Bikin Burodi Marar Yisti, kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, kamar yadda na umarce ku. Ku yi wannan a lokacin da aka ayana a watan Abib, gama a watan ne kuka fito daga Masar. “Kada wani yă zo a gabana hannu wofi.
“Ku yi Bikin Burodi Marar Yisti domin a wannan rana ce na fitar da ku ɓangare-ɓangare daga Masar. Ku kiyaye wannan rana ta zama muku dawwammamiyar farilla wa tsara masu zuwa.
Gama Ubangiji ya yi tsaro a wannan dare, domin yă fitar da su daga Masar, a wannan dare, dole dukan Isra’ilawa su yi tsaro, don su girmama Ubangiji, cikin dukan tsararraki masu zuwa.
Sa’ad da Ubangiji ya kawo ku cikin ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku, ƙasar da take zub da madara da zuma, za ku kiyaye wannan biki a wannan wata.