Bayan ka sa waɗannan riguna wa ɗan’uwanka Haruna da ’ya’yansa, ka shafe su da mai, ka kuma naɗa su. Ka keɓe su domin su yi mini hidima a matsayin firistoci.
ka kuma sa musu huluna a kansu. Sa’an nan ka ɗaura wa Haruna da ’ya’yansa abin ɗamara. Su kuwa da zuriyarsu, aikin firist kuwa zai zama nasu ta wurin dawwammamiyar farilla. “Ta haka za ka keɓe Haruna da ’ya’yansa maza.
“Kawo Haruna da ’ya’yansa maza, ka ɗauki rigunansu, man keɓewa, bijimi domin hadaya don zunubi, ’yan raguna biyu da kuma kwandon da yake da burodi marar yisti,
“Ka sa a kawo maka Haruna ɗan’uwanka, tare da ’ya’yansa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar daga cikin Isra’ilawa, domin su yi mini hidima a matsayin firistoci.
Amma Haruna da zuriyarsa su ne waɗanda suke miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa da kuma a kan bagaden turare haɗe da dukan abin da ake yi a Wuri Mafi Tsarki, suna yin kafara domin Isra’ila, bisa ga dukan abin da Musa bawan Allah ya umarta.