Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 5:18 - Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Zai kawo wa firist rago daga garke, marar lahani. Za a kimanta tamanin rago daidai da tamanin hadaya don laifi. Firist kuwa zai yi kafara don kuskuren da mutumin ya yi ba da saninsa ba, za a gafarta masa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

18 Sai ya kai wa firist rago marar lahani daga cikin garke. Za a kimanta tamanin rago daidai da tamanin hadaya don laifi. Firist kuwa zai yi kafara don kuskuren da mutumin ya yi ba da saninsa ba, za a gafarta masa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 5:18
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

yă kuma yi da wannan bijimi kamar yadda ya yi da bijimi na hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominsu, za a kuwa gafarta musu.


Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya ta ƙonawar, za a kuwa karɓa a madadinsa don a yi kafara dominsa.


“In mutum ya yi zunubi, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, ko da yake bai sani ba, shi mai laifi ne. Za a kuwa nemi hakki daga gare shi.


Hadaya ce ta laifi, ya yi laifi na abin da ya yi marar kyau ga Ubangiji.”


“Sa’ad da firist zai ɗauki ɗaya daga cikin ragunan ya kuma miƙa shi kamar hadaya don laifi, tare da moɗan mai; zai kaɗa su a gaban Ubangiji kamar hadaya kaɗawa.


in kuwa aka yi haka ba da gangan ba, kuma da rashin sani, sai duk jama’a su miƙa ɗan bijimi don hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, tare da ƙayyadadden hadaya ta gari, da hadaya ta sha, da kuma bunsuru na hadaya don zunubi.


“ ‘In hadaya ta ƙonawar daga shanu ne, sai yă miƙa namiji marar lahani. Dole yă kawo shi a ƙofar Tentin Sujada don yă zama yardajje ga Ubangiji.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ