Firistoci 4:21 - Sabon Rai Don Kowa 202021 Sa’an nan zai ɗauki bijimin waje da sansani yă ƙone shi kamar yadda ya ƙone bijimi na fari. Wannan ita ce hadaya don zunubi domin jama’a. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki21 Zai kai bijimin a bayan zango, ya ƙone shi kamar yadda ya yi da na farin, gama hadaya ce don zunubin taron jama'ar. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa’an nan sai waɗanda suka dawo daga bauta suka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Allah na Isra’ila. Wato, bijimai guda goma sha biyu don Isra’ilawa duka, raguna tasa’in da shida, ’yan raguna saba’in da bakwai, bunsurai kuma guda goma sha biyu. Aka miƙa su hadaya don zunubi. Wannan duka hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji.